fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Wani direba ya murkushe jami’in LASTMA har lahira yayin da yake kokarin kama shi a jihar Legas

Wani direba ya murkushe wani jami’in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas, Jamiu Issa, har lahira a unguwar Lekki-Ajah da ke jihar.

Direban yana tuƙi ne ba bisa ka’ida ba inda a lokacin ne Jamiu Issa ya yi ƙoƙarin kama shi saboda laifin da ya aikata amma direban ya yi cikinsa da mota.

An garzaya da Jamiu Issa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Shaidun gani da ido sun bi direban Sienna yayin da yake kokarin tserewa daga wurin. Ana cikin haka ne ma ya buge wani mutum kafin a kama shi.

Karanta wannan  Yan bindiga sun kai hari kauyen Katsina, sun bindige wasu manoma 15

An fara kai direban ofishin ‘yan sanda na Ilasan, daga karshe kuma zuwa ofishin ‘yan sanda na Ajiwe.

Masoya sun yi ta’aziyya a shafin facebook domin jajantawa jami’in da ya rasu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.