fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Wani Fasto yace mu bada kudi a yi addu’a dan ya hango jirgin shugaba Buhari zai yi hadari>>Fadar Shugaban kasa

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa wani fasto ya nemi a bayar da kudi dan ayi addu’a kar jirgin shugaban kasa yayi hadari.

 

Faston yace ya hango jirgin yayi hadari da shugaban kasa,  Muhammadu Buhari.

 

Kakakin Shugaban kasa, Femi Adesina ne ya bayyana haka inda yace faston ya nemi kudi masu yawa.

 

Adesina ya fadi haka ne a shafinsa na Facebook inda yace faston dan damfara ne.

 

Yace faston yace hadarin zai farune a karshen shekarar 2021 amma gashi bai faru ba. Yace tunda shugaban kasa Buhari ya hau mulki ake masa fatan mutuwa da ciwo amma gashi har yanzu yana aikinsa ba tare da matsala ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.