Bayan wata 2 da babban alkalin jihar Adamawa ya yi masa afuwa bisa laifin sata, an sake yanke wa matashi dan shekara 19, Mubarak Yuguda hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari bisa samunsa da laifin sake aikata sata.
An gan shi a lokacin da yake tattara kayan gida a cikin wani gini da ke kusa da ba a kammala ba inda aka sake kama shi, aka bincike shi, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu.
Da aka karanta masa tuhumar da ake masa, Mubarak ya amsa laifinsa. Daga nan ne kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari ko kuma ya biya tarar Naira 150,000.