fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Wani ma’aikacin INEC ya gayamin cewa sun taimakawa Buhari ya ci zabe a jihohi 7 a 2019, APC zata tarwatse>>Buba Galadima

Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya bayyana cewa jam’iyyar APC zata watse ta yanda ba zata taba dawowa daidai ba.

 

Buba ya bayyana hakane a sabuwar tattaunawar da yayi da manema labaran Vanguard inda yace a yanzu haka jam’iyyar ta rabu zuwa kashi-kashi.

Yace tun a baya yayi gargadin cewa Adams Oshiomhole da aka nada a jam’iyyar(dan ba zabenshi aka yi ba) zai wargazara ne. Yace wanda suka sashi ya musu aiki saboda sun san mutum ne me rawar kai shiyasa suka sashi, yace gashi kuma ta faru.

 

Yace a yanzu akwai bangaren shugaban kasa, da bangaren Tinubu, dana El-Rufai, gwamnan Kaduna da kuma na gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu. Yace Oshiomhole ba zai tana iya kai APC ko shugaban kasa kotu ba saboda suna da abinda zasu kamashi dashi, shiyasa ma yayi gaggawar amincewa da saukeshi da aka yi. Ya kara da cewa da ace ba’a hana zirga-zirgar jiragen sama ba, da tuni ya fice daga kasarnan.

Karanta wannan  An shawarci Peter Obi ya nemi naira biliyan hamsin idan har yanaso ya kayar da Tinubu a zaben 2023

 

Yace PDP nesa ba kusa ba ta fi APC suna da karbuwa wajan ‘yan Najeriya dan inba haka ba me nene yasa saida APC ta yi amfani da sojoji sannan ta ci zabe? Yace APC ba zata taba iya cin zabe ba da dan takararta ba tare da magudi ba, yace akwai maaikacin  INEC da ya gayamai cewa sun taimakawa zaben 2019 na shugaban kasa da jihohi 7 kamin yayi nasara.

 

Yace wannan rarrabuwa da APC ta yi, muddin ba’a dauki mataki me kyau ba to ba zata sake hadewa ba, ta watse kenan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.