fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Wani mabiyin addinin Hindu dan kasar Indiya ya kashe musulmi kuma ya saka hoton bidiyon kisan a yanar gizo: Wai a tallafamai da kudi dan yayi maganin musulmi

Indian Hindu kills man & posts murder online as part of fundraiser against Muslims - police
Wani mutum dan kasar Indiya, mabiyin addinin Hindu ya kashe wani musulmi sannan ya dauki bidiyon gawar ya saka a dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda ya rubuta bayanan asusun ajiyarshi na banki, ya bukaci ‘yan uwanshi masu bin addinin Hindu su tara mai kudi domin yaci gaba da wannan aiki nashi na maganin musulmi, kamar yanda ya bayyana.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Mutumin da ake kira da Shambu Lal Regar, ya samu hadin kan kusan mutane dari bakwai a cikin kasar ta Indiya da suka taramai kudin da suka kai dalar Amurka dubu hudu da dari shida da sittin da biyar, kwatankwacin sama da naira miliyan daya da dubu dari shida.
‘Yan sandan kasar ta Indiya sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mutumin ya bayyana cewa yana so yayi yaki da wani abu da musulmin kasar keyi da ake kira da jihadin soyayya, rahotanni sun bayyana cewa musulmai na jan ra’ayin ‘yan mata mabiya addinin Hindu da sunan soyayya inda daga baya suke shigar dasu addinin musulunci.
Shidai wannan mutumi an kamashi da laifin kisa, kuma hukumomi sun rufe asusun ajiyarshi na banki inda dan tsayar da kudin da mutane ke tara mai, sannan ‘yan sanda sun fara bibiyar wadanda suka aikamishi da tallafin kudi dan suma a kamasu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Mun nunawa Abba Gida-Gida Soyayya amma ya nuna mana kiyayya>>Inji Wani da aka rushewa shago a Kano

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *