fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Wani magidanci da karuwarsa sun mutu yayin da suke zina cikin mota a jihar Legas

An tsinci gawar wani magidanci da masoyinsa da suke jima’i a cikin motarsa (SUV) a Estate Jakande da ke Isolo, Legas.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa makwabta sun gano cewa mutanen sun mutu ranar Lahadi 1 ga Mayu, bayan sun lura cewa motar ta kasance a wajen har cikin daren Asabar, 30 ga Afrilu.

An bayyana sunan mutumin da Koyejo kuma an ce ya dauko masoyinsa da ba a bayyana sunansa ba ne a Isolo yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gidan danginsa da ke Jakande Estate.

Mutumin wanda IT Injiniya ne yana zaune tare da matarsa ​​a Surulere, rahotanni sun ce  ya kira abokansa ya shaida musu cewa yana kusa, kafin ya yi parking a Junction Double Star domin ya saye suya.

Karanta wannan  Yajin aikin Kungiyar ASUU ya tilasta min farautar mijin aure cikin gaggawa – Wata dalibar ‘yar shekara 20 ta koka

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa jama’ar gari sun shiga rudani bayan da suka lura cewa motarsa ​​mai lamba EPE666GE, ta kasance a wajen daga daren ranar Asabar zuwa daren Lahadi kuma a wuri guda.

Kakakin ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa binciken gawarwakin mutanen ne kawai zai iya bayyana musabbabin mutuwarsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.