fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Wani magidanci mai yara 18 a Kenya ya shirya tafiya barzahu inda ya sayawa kansa akwatin gawa karo na uku

Wani magidancj dan shekara 87 a kasar Kenya, Alloise Otieng’ Ominang’ombe ya sayo sabin akwatin gawa saboda a saka shi a ciki idan ya mutu.

Magidancin mai yara 18 ya bayyana cewa yayi hakan don ya tunatar da mutane cewa ita mutuwa fa ba’a sanin lokacinta kuma masu wayau ne suke shirya mata.

Akwatin gawar ya kasance na uku daya saya domin ya taba saya a shekarar 2009 da kuma 2012.

Kuma yace ya sayi sabo ne saboda an dena yayin tsaffin akwatin gawar daya saya a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.