fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Wani magidanci tare da yaronsa sun mutu a cikin wata rijiya a jihar Kano

Wani magidanci dan shekara 60 Malam Bala da yaronsa Sanusi Bala dan shekara 35 sun mutu a cikin rijiya a jihar Kano ranar talata.

Wannan lamarin ya faru ne a Sabon Garin Bauchi dake karamar hukunar Wudil kamar yadda mai magana da yawun hukunar dake kashe gobara, Alhaji Saminu Abdullahi ya bayyana.

Inda yace wani bawan Allah ne Idris ya kira su a waya ya sanar dasu cewa wani mutun da yaronsa sun makale a cikin a cikin rijiya, inda suka hanzarta zuwa domin su ceto su.

Kuna yace an kira mutumin da yaron nasa ne don su haka rijiyar kuma sun kammala hakata sai yaron ya koma ya sake gyarata wanda anan ne ya makale har mahaifin yaje ceto shi shima ya makale.

Karanta wannan  Sanatoci sunyi watsi da kudurin kafa dokar karba karba da zata baiwa kowace kabila damar shugabanci a Najeriya

Hukumar tayi nasarar ceto su amma duk da haka sai da suka bakunci lahira, inda hukunar tace rashin iskar da zasu yi numfashi a cikin rijiyar ne yasa suka mutu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.