fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Wani matashi dan Najeriya yarasa ransa a sakamakon kamuwa da cutar Covid-19 a kasar Amurka

Yadda wani matashi dan Najeriya ya mutu a sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus a kasar Amurka.

Matashin dai mai shekaru 25 mai suna Bassey Offiong dalubi ne wanda yake karanta chemical engineering a kasar Amurka wanda ya rage befi sati ya kammala karatunsa na digiri ba, kamar yadda jaridar Detroit News suka rawaito.

A cewar yar uwar mamacin Asari Offiong ta bayyana cewa dan uwanta ya fada mata cewa yana jin numfashin shi yana daddaukewa sannan ga zazzabi mai zafi, wanda duka alamomine dake nuna ya kamu da cutar Covid-19.

Dan uwan nata ya fada mata cewa ya jajje gwaje-gwaje na cutar a Kalamazoo amma sai dai ya dawo a sakamakon kin yi masa gwajin da asbitin suka kiyi.

Sai dai yar uwar tashi bata bayyana sunan asbitin da suka ki yimasa gwajin.

A karshe jami’ar ta taya yar uwar dalubin alhinin rashin dan uwanta sannan a rahotan da Jami’ar da dalubin yake karatu hukumar Jami’ar ta bayyana mutane uku ne suka kamu da cutar Covid-19 a ranar juma’ar data gabata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.