IDAN KA KI JI….
Wani Matashi Ya Ki Komawa Gida Bayan Ya Yi Asarar N75k A Cacar Wasannin
Daga Aliyu Adamu Tsiga
Rahotanni sun bayyana cewa wani matashi ya yi amfani da Naira 75,000 wajen cin karo da juna a wata cibiyar cacar wasanni amma sakamakon ya kasance mai ratsa zuciya a yayin da bai ci gasar ba.
Mutumin ya rasa duk kuɗin da ya tafi da shi, an bar shi cikin ɓacin rai a cibiyar wasannin har ma ya ƙi komawa gidan su.
A wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta na yanar gizo, ana iya ganin yaron riƙe da tulin tikitin da aka yanke wanda ya yi sanadin asarar naira 75.
Ya fita waje ya zauna a bakin ƙofar shiga gidan cacar wasannin, inda yayi ƙoƙarin hana kansa zubar da hawaye amma abun ya ci tura yana tunanin me zai yi bai san lokacin da ya fashe da kuka ba.