fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Wani matashi ya koka da korarsu daga aiki inda aka dauki Zahara Buhari aikin daga baya

Jaridar Signalng.com da ake wallafawa a yanar Gizo ta ruwaito wani ma’aikacin wucin gadi na hukumar dake kula da farashin albarkatun man fetur ta kasa, PPPRA yana korafi kan sallamarsu daga aiki da aka yi amma aka dauki diyar shugaban kasa, Zahara Buhari aikin dindindin.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Mutumin da jaridar bata wallafa sunanshi ba ya bayyana mata cewa, Suna fama da matsala a boye kuma babu wanda zai sauraresu, ni ma’aikaci PPRA ne na wucin gadi daya shafe shekaru 7 yana aiki inda aka mana alkawarin daukar aikin dindindin. An kawo Babban Sakatare Abdulkadir Umar Saidu daga NNPC zuwa PPPRA. Da zuwanshi aiki ya kore mu mu 34 daga aiki. Ya mana Alkawarin cewa idan zasu dauki aiki za’a fara da mu.

Karanta wannan  'Yan bindiga sun sako mutane shida hadda yaro dan shekara guda cikin fasinjojin jirgin kasa bayan Sheik Gumi ya masu wa'azi

Amma an yi wani daukar aiki a boye a tsakanin watannin Nuwamba da Disamba wanda yawanci Hausa Fulanine aka dauka aikin, sun bauwa Sanatoci damar kawo ma’aikata ba tare da kula damu ba. Cikin wanda aka dauka hadda diyar shugaban kasa, Zahara wadda aka baiwa mukamin mataimakin Manaja.

Ya bayyana cewa tana cikin matsala saboda yana da iyali da iyaye da yake kula dasu


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.