fbpx
Saturday, September 23
Shadow

WANI MATASHI YA TUƘA KEKE DAGA BAUCHI ZUWA ABUJA DOMIN GANIN MINISTA WIKE

WANI MATASHI YA TUƘA KEKE DAGA BAUCHI ZUWA ABUJA DOMIN GANIN MINISTA WIKE

 

Matashin ya bayyanawa Jaridar Dokin Ƙarfe TV cewa tsakaninsa da gwamna Wike amana ce domin shi ne ya ɗauki nauyin karatunsa na Jami’a tun zamanin ya na gwamnan Jihar Rivers a shekarar 2017. Kamar yadda ya bayyana cewa:

 

“Na Yi Amfani Da Keke Daga Bauchi Zuwa Abuja Na Kai Ziyarar Girmamawa Ta Musamman Ga mai gidana mai girma Ministan Abuja Nyesom Wike. Na kai masa wannan ziyara ne saboda yaba masa kan ƙoƙarin da ya ke kan cigaban siyasa a Nageriya.

 

Mista Wike shi ne ya ɗauki nauyin karatuna har na gama Jami’a, na ɗauke shi a matsayin jagorana, madubin dubana, abin alfaharina”. Inji shi.

 

Dangane da asalin alaƙarsu da Mista Wike kuwa, matashin ya bayyana cewa: ” a 2017 lokacin ya na matsayin gwamnan Jihar Rivers mai gidana Alhaji Mai Sundu abokinsa ne mu na zuwa masa aiki tare da shi. Wata rana gwamna Wike da babban lauyan Jiha sun zo neman mai gidana su ka tambaye ni ina ya ke sai na faɗa musu ya tashi yanzu. Sai ya sake tambaya ta ni mai nake yi yanzu sai na faɗa musu cewa ina duba aiki ne ina ɗaukar sunayen ƴan aikin.

Karanta wannan  Za a fara gwajin riga-kafin cutar HIV a Afirka ta Kudu

 

Sai gwamna ya sake tambaya ta ko na yi karatu kuma miye matsayin karatun, sai na ba shi amsa da cewa takardar sakandire ce da ni sai ya sake tambaya ta ko ina son cigaba da karatu sai na amsa masa da eh! Washe gari sai Ogana Alhaji Ibrahim ya ce mu je gidan gwamnati, mu na zuwa mu ka je ofishin babban lauyan gwamnatin Jiha take ya ba ni tallafin karatu da takardar fili ya ce inji gwamna. Wannan ya faru a ranar 14 ga watan 4 2017″. Ya ce.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *