fbpx
Saturday, June 25
Shadow

Wani Mejo Din Sojan Nijeriya Ya Yi Wa Kansa Kisan Gilla A Kaduna

Wani Mejo Din Sojan Nijeriya Ya Yi Wa Kansa Kisan Gilla A Kaduna

Wani jami’in sojan Nijeriya mai suna Mejo Udiadenye Jerimiah Udiadenye ya yi kansa kisan gilla a jihar Kaduna.

Saidai bayan kashe kan sa da Sojan ya yi, wasu rahotanni sun yi ta yaduwa kan cewa jami’in sojan ya kashe kansa ne saboda tuhumar da kotun sojoji ke yi masa kan laifi da ya yi.

Saidai daga bisani hedikwatar rundunar tsaron ta kasa ta fito ta musanta batun cewa tuhumar da take yi masa ne ya sa ya kashe kansa, inda ta kara da cewa a tarihin mamacin ma bai taba fuskantar tuhuma daga kotun sojojin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.