Mosugu Ezekiel Atebi da ‘ya’yansa biyu, Joana da Jason, sun mutu a wani mummunan hatsarin mota.
An tattaro cewa hatsarin ya afku ne a kan hanyar Keffi zuwa Abuja a ranar Juma’a, 15 ga Afrilu. An yi jana’izar baban da yara a yau Juma’a, 22 ga Afrilu.
A cewar Petra Akinti Onyegbule, tsohon babban sakataren yada labarai na gwamna Yahaya Bello, kwanaki kadan kafin afkuwar hatsarin, marigayin ya binne dan uwansa, Barista Tibileri Mosugu, wanda aka kashe a harin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna.
