fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Wani mutum ya cinnawa gidan surukansa wuta a jihar Jigawa

Wani mutum mai shekaru 40, Ibrahim Musa ya cinnawa gidan surukarsa wuta a kauyen Kuzoyara, karamar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa.

Bincike ya nuna cewa mutumin ya kona gidan surukinsa ne kan rashin matar ta komawa gidansa bayan rabuwar wucin gadi da shi.

An yi zargin cewa ya shiga gidan dangin matar ne a daren Litinin lokacin da suka je ziyarar ta’aziyya kuma ya cinnawa gidan wuta.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, Asp Lawan Shiisu Adam ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Karanta wannan  Zan iya rantsuwa da alkur'ani cewa Atiku ne ya lashe zaben shekarar 2019, cewar Buba Galadimar

Ya ce wanda ake zargin ya je gidan surukinsa da ke kauyen Kuzoyara ya cinna masa wuta.

A sakamakon haka, wani bukka mallakar surukarsa ta kone kurmus, amma ba a rasa rai ba.

Adam ya ce an kama wanda ake zargin yayin da ake ci gaba da bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.