fbpx
Monday, March 1
Shadow

Wani mutum ya dabawa kanen sa, Sulaiman wuka har lahira

Mai laifin (Kadir)

Wani mutum mai suna Kadir ya gudu bayan da ake zarginsa da daba wa kanensa, Suleiman wuka har lahira a Auchi, karamar hukumar Etsako ta Yamma dake Jihar Edo.

 

An bayyana cewa rikicin ya fara ne a safiyar Juma’a, 19 ga Fabrairu, lokacin da Suleiman ya tsawata wa matar Kadir saboda rashin girmama mahaifiyarsu.

 

Kadir, wanda ba ya gida lokacin da lamarin ya faru, ya umarci kanen nasa da ya tsawata wa matarsa a lokacin da ya dawo.

Sai dai mahaifiyarsu ta shiga tsakani kuma ta sasanta rikicin tsakanin ’yan uwan ​​biyu.

An ce Kadir ya sake tayar da maganar a ranar da yamma kuma, mahaifiyarsu ta sasanta lamarin.

Suleiman ya ajiye batun inda ya nufi wajen kasuwancin sa na yau da kullun, sai dai ana tunanin daga baya Kadir ya bi shi zuwa inda ya tafi da yamma, kuma ana zargin ya daba masa wuka ya gudu.

Wanda aka kashe (Suleiman)

Nan take aka garzaya da Suleiman zuwa asibiti a daren Juma’a inda ya mutu a safiyar ranar Asabar sakamakon raunin da yaji.

Kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar Edo, Princewill Osaigbovo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce mamacin ya mutu ne a asibitin St. Jude, kuma sun fara bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *