fbpx
Monday, December 5
Shadow

Wani mutum ya hana diyarshi amsa tambayar da akayi mata daga makaranta a kasar Ingila na cewa ta rubutawa iyayenta wasika zata shiga addinin musulunci

Father refuses to let stepdaughter, 12, do homework about converting to Islam
Wani uba a kasar Ingila ya hana diyarshi yin aikin gida da aka bata daga makaranta saboda an tambayeta ta rubutawa iyayenta wasika akan tana son karbar addinin musulunci, kamar yanda ake ganin hotonnan na sama yana dauke da tambayar da aka yiwa yarinyar ‘yar shekari 12 akace taje gida ta amsa.

Koda akayi arashi mahaifinta ya ga wannan tambaya da aka yi mata sai ya hanata amsa tambayar
Sannan kuma ya tafi makarantar dan yaji ba’asi akan dalilin da yasa za’a sa ‘yarshi ta rubuta musu cewa zata canja addini, mutumin me suna Mark ya bayyana cewa baya inkarin cewa a fahimtar da yara addinai daban-daban tunda yasan cewa hakan yana cikin tsarin koyarwa na kasar.
Amma abinda ya daure mishi kai shine yanda za’a tambayi yarinya ‘yar shekaru 12 ta rubutawa iyayenta cewa zata canja addini zuwa Musulunci, maimakon haka kamata yayi a fahimtar da ita menene musulunci kuma a sanar da ita duk tarihin daya shafi addinin, ya kara da cewa Hakkinsune iyaye su tarbiyyan tar da yara yanda ya dace har su kai lokacin da zasu mallaki hankalin kansu daga nan duka irin shawarar da zasu yankewa rayuwarsu babu wanda zaice danme?
Koda mutumin yaje makarantar, kamar yanda Metro UK suka ruwaito sai malaman makarantar suka tabbatar mishi da cewa wannan tambaya da akawa diyarshi yana cikin tsarin koyarwa na kasa, kuma suka nuna mishi irin wannan tambaya da aka yiwa yaran akan addinin kiristanci da na Hindu.
Mutumin dai ya dauki hoton wannan tambaya da aka yiwa diyar tashi ya saka a yanar gizo, kuma ta dauki hankulan mutane da dama inda aka bayyana ra’ayoyi mabanbanta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  'Yan sanda sun kama matar da ta binne jaririn da ta haifa a Jigawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *