fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Wani mutum ya kashe kansa ta hanyar rataya

Wani mutum dan kasar India, Devendra Singh ya kashe kansa ta hanyar rataya a ofishinsa dake Legas.

 

Lamarin ya farune ranar Juma’a inda direbansa ya kaishi ofis kamar yanda ya saba, amma an fara damuwa ne bayan da lokacin tashi aiki yayi amma be fito daga Ofishin nasa ba.

 

Direban ya leka ta taga yaga ko zai ganshi amma sai ya hango gawarsa a rataye, ya kira abokinsa inda suka kaiwa ‘yansanda rahoto.

 

Da karfi aka bude kofar Ofishin nasa aka fito dashi, Tuni dai an fara bincike kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.