fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Wani Mutum Ya Kashe Yarinya ‘Yar Shekaru 7 a Jos

Yarinyar ‘yar shekara bakwai, Zakiya Auwal, ta mutu a hannun wani mai suna Ismail Ibrahim a Unguwan Rimi da ke karamar hukumar Jos-Arewa a jihar Filato.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mansur Sha’aban, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kara da cewa an cafke wanda ake zargin kuma an fara bincike a kan lamarin.
An ce wanda ake zargin ya bugi yarinyar sau da yawa da dutse a kanta a cikin gidan mahaifinta.
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 4 na yamma lokacin da mahaifiyarta ke barci kuma mahaifinta ya fita.
A cewar wani mai shaida, Haruna Auwal, wanda yaya ne ga mamaciyar, wanda ake zargin ya bi ‘yar uwar tasa a lokacin da za ta fita daga gidansu.
“na kasance a waje lokacin da wanda ake zargin ya tunkari yankinmu yana neman mutane su ba shi kudi ko kuma a kashe su. Ya rike wani mutum sai mutumin ya bashi N50 sannan ya bashi damar wucewa.
“Bayan wasu lokuta, ya bi yara da yawa ciki har da ni. Dukkanmu mun gudu amma sai ya shiga gidanmu kuma kwatsam ya rike kanwata yayin da take fitowa daga gida.
“Ya dauki dutse, ya ture ta kasa ya buge ta a kai a kai har sai da kwakwalwarta ta fito. Ta mutu nan take ’’, in ji shi.
Mahaifin marigayiyar, Auwal Bello Zakari, yayin da ya ke nuna kaduwa game da lamarin ya ce bai san wanda ake zargin ba kuma ya yi kira ga hukuma da ta tabbatar an yi adalci a cikin lamarin.
An ruwaito cewa an kai wanda ake zargin zuwa ofishin ‘yan sanda na Unguwan Rogo amma daga baya aka sauya shi zuwa yankin ‘ A ’ na yan sandan Jos.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Tekun Legas ya tafi da dalibai hudu da suka je murna bayan sun lashe jarabawar WAEC

Leave a Reply

Your email address will not be published.