Rundunar ‘yan sanda a jihar Yobe ta cafke wani mutum da ake zargi da yi wa wata tsohuwa‘ yar shekara 90 fyade a cikin gidanta.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Dungus Abdulkarim shine ya shaida hakan ga manema labarai a jihar, inda ya ce wanda ake zargin, Mohammed Faruk mai shekaru 35 ya aikata laifin da ake zargi sa dashi a garin Gadaka, inda ya kutsa hardakin tsohuwar mai shekaru 90 tare da haike mata.
Mista Abdulkarim ya ce wanda ake zargin ya amsa aikata laifin ne bayan da wani rahoton likita ya tabbatar da cewa an yi wa matar fyade.
A cewar Jami’in “A halin yanzu ana gudanar da bincike a kan lamarin sannan kuma za’a mika mai laifin zuwa sashin bincike na hukumar ‘yan sanda na jihar don gudanar da bincike cikin tsanaki kafin gurfanar dashi a gaban kotu.