fbpx
Friday, December 2
Shadow

Wani Shehin malami daga kasar Saudiyya ya gina masallaci a Kano

Wani shehin malami daga kasar Saudiyya ya ginawa al’ummar karamar hukumar Bebeji masallaci, a jiyane shehin malamin tare da tawagarshi suka sauka a jihar kanon inda ya bude masallacin.

Dan majalisar wakilai da aka dakatar dake wakiltar mazabar kiru da bbebejine ya bayyana haka, gadai abinda ya fada:

Jiya mun yi dacen samun baki na musamman a garin mu na Kofa Karamar Hukumar Bebeji Kano daga Saudi Arabia wanda suka hada da wanni Babban Abokin mu Sheik Saleh Al Subaihi. Ya zo ne don ganin aiki da assasa tubalin ginin Masallaci dayayi wa jamaar kofa. Wannan bako ya samu rakiyar Manyan Malamai na Kano, wanda suka hada da Sheik Dr  Abdullahi Pakistan, Sheik Abdulwahab Abdallah, Sheik Mahmud Arafat, Mallam Dr Kabiru Kofa,  Ustaz Sani Darma, Malam Abdulsalam Babangwale, Malam Zakariya Ishaq, Malam Ahmed Ahmed Kura, Dr Aliyu Musa Aliyu da wasunsu. Bayan gama shidindimu sun yi mana Adu’o’i na musamman akan zaluncin da akai mana na Dakatarwa daga Majalisa da fatan Allah ya bamu rinjaye akansu, Allah ya baiyana  gaskiyar lamarin ya tsaremu daga sharrinsu.
Ba abin da zamuce sai godiya ga Allah da su wadannan baki, Masha Allah.”
Muna fatan Allah ya sakamai da Alheri

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Aisha Buhari ta janye kararda ta kai Aminu Muhammad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *