Shugaban karamar hukumar Magama a jihar Neja Alhaji Safyanu Yahaya dake Jam’iyyar PDP ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Sauya shekar shugaban na zuwa ne mako daya kacal bayan da jam’iyyar ta fadi babban zabe na majalisar wakilai wanda jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta lashe.
Sanarwar ta fito ne ta hannun Shugaban jam’iyyar APC dake mazabar Magama a jihar Neja.