fbpx
Monday, March 1
Shadow

Wani Tsohon Dan majalisa A jihar Nasarawa ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Dakta Haruna Kigbu, wani tsohon dan majalisa ne wanda ya wakilci Mazabar Lafia / Obi A Majalisar wakilai ta Tarayyar Najeriya, Dan majalisar a ranar Asabar, ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Kigbu ya sauya sheka ne tare da dubban magoya bayansa a garin lafiya dake a jihar Nasarawa.

Da yake karbar sabbin mambobin da suka sauya sheka cikin jam’iyyar, Mista John Mamman, Shugaban riko na jam’iyyar APC a jihar, ya bayyana farin cikin sa game da Dubbunan tsoffin mambobin jam’iyyar PDP da suka hambarar da tafiyar Jam’iyyar inda suka dawo jam’iyyar APC.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *