fbpx
Friday, June 9
Shadow

Wannan shine saurayin daya damfari budurwansa a garin Zariya Dubu 45

Daga Barrister Nuraddeen Isma’eel

“Wata budurwa mai suna maryam mairainiyan Allah, mahaifin ta ya dade da rasuwa, haifaffiyan garin zariya. “Inda ta yarda da wani saurayin ta da suka hadu a yanar gizo, ya umarci da ita budurwan tayi masa iso ga iyayenta zai zo har gida a yi maganar fara nemanta.”

“Budurwa mayam tace ita dai sun Dade suna soyayya a iya yanar gizo, wannan ne ganin shi ido da ido na farko, “inda ya ce mata Dan Kaduna shi toh” ita a kan haka ta yarda.”

“Bayan ya zo wurin ta, maryam ta hada masa goma sha tara na arziki na tarba, kuma nan wuri guda saurayi ya tsaya ya cinye duk abidan aka hada masa, kama na ciye-ciye da tande-tande.”

“Saurayi baiyi wata-wataba, ya ka da baki cewa! Zai siyawa maryam wayar salula ta zamani wacce takai ta dubu 45 haka.”

Bugu da kari Saurayi Hamisu, nan yake tambayan maryam a ina ake sayar da wayoyi ? Sai budurwa maryam take bashi amsa cewa! Akwai Wanda suka saba suna sayan waya a hannun sa, kuma yana da sauki.”

“Hakan ya kara bude wani sabon fai-fai ne, da shi Wanda akaje za’a siya waya a hannun shi ya yarda da maryam, saboda sun dau lokuta suna harkan arziki.”

Karanta wannan  Karfin Hali, Bidiyon yanda aka kama barawo a barikin sojoji

Rahoto ya cigaba da bayyana mana cewa! aka je wurin mai sayar da waya ya dauki waya ta dubu 45 aka baiwa saurayi, sai shi saraurayi yace zai yiwa mai sayar da wayan tiransfa din kudin shi idan suka dawo gidan su maryam saboda ya bar wayan da zai masa tiransfa cikin caji a dakin da aka sauke shi, “Mai sayar da waya ya yarda da hakan, koba komi ya wayi maryam.

“Dawowan su tare da saurayin gidan su maryam ba wuya, sai saurayi yace maryam ta bashi wayan da aka amso ta dubu 45, maryam ta dau waya ta bashi biyo bayan amsan waya sai saurayi yace zai je masallaci a domin yin sallah, daman cewa yayi zai kwana daya a gidan su maryam din.”

“Fitar saurayi ba wuya a domin zuwa masallaci tare da wayan da aka karbo daga hannun mai siyarwa, tunda saurayi ya fita ba’a kara saka shi a ido ba.

“A don haka muna rokon al’umma dasu taya mu yada Wannan rubutun a domin cafke Wannan mazanbacin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *