
Akwai wasannin motsa jiki kala-kala da akeyi, wasu dan neman suna, mafi yawanci kuma dan nishadi, wasu kuma dan neman kudi,a lokuta da dama masu wasan da wadanda ke kallon wasan sukan kasance cikin nishadi, saidai kowane irin wasa yana da irin hatsarin dake tattare dashi, wanda idan masu yinshi basu bi a sannu ba sai kaga an samu mummunan ciwo ko kuma ma har zai iya kaiwa ga mutuwa.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
A cikin wasanni da akeyi, musamman wanda duk Duniya ta yadda dasu, wanda aka bayyana, da yafi kowane hadari, shine tseren keke. Mafi yawancin hadurra dake kaiwa ga ciwo da ake samu a tseren keke, sauran kekunan dake kusa da mutu ne ke haddasasu, mutum shi kadai ba lallai bane ya fadi, amma na kusa dashi zai iya afkamishi a kowane lokaci.

Na biyunsu shine wasan kwallon kafa, Kwallon kafa ta shigo a na biyu saboda yawan ciwukan da ake ji lokacin bugata da kuma yawan ‘yan wasan dake cikin fili suke bugata, wani bincike na masana ya bayyana cewa a wasan kwallon kafa a kwai kashi saba’in cikin dari na yiyuwar mutum ya kamu da ciwon farfadiya lokacin da yake bugashi, amma a sauran wasanni kashi biyarne kawai cikin dari.

Na ukunsu shine wasan damben boksin wanda shi dukanku masu wasan neman wallen dan uwanka kake ka kaimai naushi, wani bincike da akayi ya bayyana cewa kashi casa’in cikin dari na masu wasan damben boksin na karewa da ciwon kwakwalwa.

Daganan kuma sai wasan da ake cewa da turanci Gymnastics, shi wannan wasa asalinshi sojojine akewa horo dashi, saboda anaso aga yanda mutum cikin yanayi na tashin hankali zai samu nutsuwa da daidaito da kuma kwan karfin zuciya, amma daga baya an amince a rika wasan a wasannin bazara na Olympic, zakaga mutum yana tsalle sama yana wulkitawa yana durowa akan wani dan sililin abu, hadurran dake tattare da wannan wasa sun hada da balla wuya, kwakwaso, agara da, Hadari mafi muni da aka taba samu a wannan wasa na Gymnastic shine na wata me suka Julissa Gomez a shekarar 1988, tana atisaye, tayi sama-sama ta fado ba daidaiba, ta balla kashin wuya, shine ajalinta, dan har ta mutu bata warkeba.

Wasan hawa kan saa kayi kokarin darewa akanshi na tsawon lokacin da zaka iya, a yayinda shi kuma zai ta tutsu dakai. yana kokarin kadoka, a shekarun baya masu irin wannan wasa basa saka kariyar komai, amma saboda hadarurrukan da aka rika fuskanta, dole tasa suka rika saka rigar kariya. ciwukan da irin masu wannan wasa suke karewa dashi sun hada da jin ciwo a wuya, kai da fuska, wasu kuwa har farfadiya ke kamasu.

A yakin Tamil Nadu na kasar Indiya, akwai wani wasa da saa da akeyi wanda ke da hadarin gaske, ana kiranshi da sunan JALLIKATU, kusan mutane fiye da dari biyu sun mutu sanadiyyar wannan wasa cikin shekaru ashirin da akayi ana yinshi, saboda irin halin wahalarwa da ake saka dabbobin da ake wannan wasa dasu yasa masu rajin kare hakkin dabbobi a kasar ta Indiya suka yi zanga-zanga dole tasa aka hana yin wannan wasa. Shi dai wannan wasa yakan kasancene tsakanin mutum da dabbar, kuma ana yinshine lokacin da aka samu amfanin gona yayi kyau, dan murna, mutum zaiyi kokarin rike san na tsawan wani lokaci da za’a dibar mishi, ba tare da san ya kucceba, ko kuma ya rikeshi, ya jashi zuwa wani guri da za’a dibar masa.

Wannan wani wasane da akeyi da shanu a kasar Andulus, wasan ya samo asaline lokacin ana dauko shanu daga inda suke daure ana kiwonsu zuwa inda za’a yankasu, a akan hanyar kaisu inda za’a yankasune, sai matasa su rika shiga cikinsu suna gudu tare dan nuna bajinta, daga baya sai hakan ya zama wasa da ake yi, lokaci zuwa lokaci, a duk shekara, an kiyasta cewa kimanin darine ke jikkata dalilin wannan wasa.

Sai kuma wasan yin nutso cikin ruwa, shima wannan wasa yana da hadarin gaske saboda akwai wasu ma’adanai dake karkashin ruwa da idan akayi rashin sa’a zasu iya illata mutum.

Sai kuma wasan hawan doki, mutane da dama hawan doki na birgesu, saidai shima an sakashi cikin jerin wasanni masu hadari a Duniya, akwai harbin dokin dake da illar gaske, sai kuma dokin zai iya taka mutum, da kuma yin tutsu da mutum lokacin da yake kanshi.

Sai masu wasan hawa sama su fado, ko kuma ‘yan sama jannati, irin wannan wasa ana samun wani guri me tsawon gaske, gini ko dutse a hau can kololuwarshi sannan mutum ya diro kasa, shima wannan wasa yana da hadarin gaske.
Listaka/Forbes
A nan gida Najeriya mu samman a Arewa, muna da wasanni masu hadari da suka hada da.
Langa.
Danbe.
Kokawa.
wasan jifa.
Tsere.
Dadai sauransu
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});