‘Yan Bindigar sun kashe matar me suna Sadiyya Idris me shekaru 25 da diyarta me shekaru 4.
Rahotanni sun nuna cewa, ‘yan Bindigar baau dauki komai ba bayan kisan.
Mataimakin gwamnan jihar, Samaila Yombe ya kaiwa iyalan mamatan ziyara inda ya musu ta’aziyya tare da Alkawarin daukar mataki kan lamarin.
Mijin matar, Hakilu Muhammad wanda telane yana jin lamarin ya yanke jiki ya fadi, tuni an.garzaya dashi Asibiti.