fbpx
Wednesday, February 24
Shadow

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe wani Manomi da jami’in yan sa-kai a Jihar Ondo

Wasu mutane biyu da ake zargin makiyaya ne sun harbe wani manomi da jami’in yan sa-kai a Ago Sanusi da ke kan titin Ute a Owo, hedkwatar karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

An bayyana cewa cewa makiyayan sun yi jami’an Amotekun kwanton bauna a cikin dajin.

Wata majiya ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun kai harin ne da misalin karfe 2:00 na safiyar ranar Laraba, dauke da muggan makamai, ciki har da bindigogin AK 47.

Kwamandan Amotekun Corps a jihar Ondo, Adetunji Adeleye ya tabbatar da mutuwar mutanen biyu ga manema labarai a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Ya ce mutanen garin ne suka sanar da jami’an Amotekun game da harin, ya kara da cewa wadanda ake zargin sun kona wata motar Amotekun da ke ajiye a kauyen kuma hakan ya ba mazauna kauyen tsoro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *