fbpx
Tuesday, January 19
Shadow

Wasu daga cikin tarihin Ronaldo da Lionel Messi,Mohammed Salah da Neymar suka karya

Tauraron dan wasan kasar Portugal dake taka leda a kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo nq daf da zama dan wasan daya mafi yawan kwallaye a tarihin tamola, yayin da yanzu kwallayen nashi suka kai 759 dai dai dana Josef Bican.

Ronaldo ya karya kuma ya kafa tarihi da dama a harkar tamola, shin ko ka san cewa shima akwai tarihin shi da wasu zakarun yan wasa suka karya?. Karanta kaji wasu daga cikin su.

Na farko dai shine babban abokin hamayyar Ronaldo, Messi wanda ya karya tarihin Cristiano na lashe kyatar Golden Booth bayan daya lashe 6 kuma yafi CR7 da guda biyu.

Sai Mohammed Salah wanda shi kuma ya karya tarihin Ronaldo na zira kwallaye masu yawa a kaka guda na gasar Premier League a shekara ta farko daya fara buga gasar , inda shi yaci kwallaye 32 a wasanni 36 kuma yafi Ronaldo da guda wanda shi yaci kwallaye 31 a wasanni 34 a kakar 2007/08.

Sai Neymar wanda shi kuma farashin sa yafi daraja wurin canja sheka bayan daya koma PSG a farashin yuro miliyan 222, sai shi kuma Ronaldo ya koma Juventus a farashi kusa yuro miliyan 100.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *