fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Wasu daga cikinmu rabonsu da Isilamiya tun da suka shiga makarantar kwana: Mu koma makaranta

Wannan wani kirane da wani sanannen bawan Allah dake fadakarwa a dandalin sada zumunta da muhawara na Twitter me suna Mustafa yayi akan neman Ilimin addini, lura da irin yanda zamantakewar al’umma yanzu take da zaka rika jin abubuwan da tunaninka ma bazai taba tunano maka suba amma kaji sun faru a zahiri.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Yayi maganar ne kamar haka:

“Wasu daga cikin mu tun lokacin da suka shiga makarantar(Boko) manya ta sakandare ta kwana suka daina zuwa makarantar Isilamiya, A neman Ilimi babu girman kai, Har yanzu bamu makaraba, zamu iya komawa makaranta mu koyi addininmu, Kar mu rika ibada da duhun kai, mu tuba”

Karanta wannan  'Yan Bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa sun ce zasu fara kashesu

Wannan kira nashi ya dauki hankulan mutane sosai inda da yawa suka yadda da wannan magana da yayi.

Amma wani lokacin fa hadda zamani duk da yake cewa akwai rashin ilimin yana tafiya tare da wasu ayyukan ashsha da ake aikatawa amma irin neman ilimin da mutane keyi a yanzu boko da arabi kusan za’ace ba’ayi irinshi a shekarun bayaba.

Sai dai Allah yasa mu dace, ya kuma shiryemu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.