fbpx
Saturday, August 8
Shadow

Da Dumi-Dumi: Wasu Dage Cikin Gidajen Mai Na Abuja Sun Fara Sayar Da Man Fetur A Sabon Farashi

Gidajen mai a birnin tarayya Abuja sun fara sayar da man fetur a sabon farashin da gwamnatin tarayya ta kayyade na Naira 143, kamar yadda aka sanar da faraway daga ranar 1 ga watan Yuli 2020.

Binciken da tawagar manema labarai suka yi ranar Alhamis a yanki Abuja ya nuna cewa, gidajen mai dake a unguwannin Wuse, Gwarimpa, Maitama, Wuye, Asokoro da Karmo duk sun fara sayar da man fetur din a sabon farashin da gwamnati ta sanya.
Alhaji Suleiman Yakubu, jami’in watsa labarai na kungiyar masu sayar da man fetur na ‘Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN)’ ya bayana wa manema labarai cewa, gidajen mai da yawa sun fara sayar da man fetur din a sabon farashin yayin ake sa ran sauran gidajen mai da basu fara ba su fara nan gaba kadan.
“Muna goyon bayan gwamnati da kudurorinta muna sane da cewa, gwamnati na kokarin taimakon talakawa ne a harkokinta, haka kuma bangaren harkar samar da man fetur ya samu matsala tun da aka fara fuskantar annobar cutar korona a kasar nan” inji Yakubu.
A ranar 1 ga watan Yuli 2020 sabon farashin da gwamnatin tarayya ta sanya na Naira 143 ya fara aiki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *