fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Wasu Fusatattu a jihar Imo sun cinnawa wasu barayi wuta da aka kama Da laifin sata

Wasu mutane biyu da ake zargi da ‘yan fashi da makami ne dubun su ta cika a loacin da aka cafke su  bayan sun yi wa wata mata fashin wayarta ta Android a garin Akuma da ke karamar Hukumar Oru ta Gabas a Jihar Imo.

Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a cikin Kasuwar Afor Akuma, inda matar ta je sayen wani abu.

Wasu da suka shaida mana yadda lamarin ya faru sun bayyana cewa barayin sun tare matar ne inda suka umarce ta da ta basu wayarta sai dai matar tai ta maza inda ta fallasa su wanda ya sanya jama’ar dake gurin an kara.

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun dauke manoma shida a jihar Borno

Anyi bata kashe da ‘yan fashin kafin daga bisani a cafke su yayin da mafusatan da suka dakume barayin suka cinna musu wuta sai dai wasu rahotanni sun shaida cewa a kwai daya daga cikin barayin da ya tsere.

Jami’in hulda da Jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ya bayyana cewa harzuwa wannan lokaci rundunar bata samu cikakken bayani game da lamarin ba.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.