fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Wasu fusatattun matasa sun bankawa wani mutum wuta da ake zargi da satar igiyoyin lantarki a Akwa Ibom

Wasu fusatattun matasan al’ummar Obot Idim da ke karamar hukumar Ibesikpo Asutan a jihar Akwa Ibom sun kona wani da ake zargin barawon wayoyi lantarki ne.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 18 ga watan Afrilu, a kan hanyar Aka Nnung Udoe, mai tazarar kilomita kadan daga Uyo, babban birnin jihar.

Wani faifan bidiyo da LIB ta gani ya nuna matashin yana rokon a yi mashi afuwa amma sam sukai banza da shi.

A cewar Kwamared Efremfon Bassey, dan kungiyar matasan yankin, matasan yankin sun yi wa barayin kwanton bauna, sakamakon lalata igiyoyin wutar lantarki da suke yi.

Karanta wannan  Matashi dan shekara 16 ya kashe kansa a jihar Kano

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda (CP), Mista Amiengheme Andrew, ya gargadi al’umma yankin kan su daina daukar doka a hannunsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.