fbpx
Saturday, June 25
Shadow

Wasu fusatattun mutane sun kashe barawon mota a jihar Katsina

Wasu fusatattun mutane sun kashe wani barawon mota a karanar hukumar Charanci dake jihar Katsina ranar asabar.

Barayin su biyar ne suka sace motar a hannun Alh. Usman Abdulmumin yayin dayaje lura da gonarsa, kuma motar Honda ce mai farashin naira miliyan 2.6.

Hukumar ‘yan sanda sun kawo dauki bayan da suka samu labarin, amma barawon dake tuka motar ya nemi ya tsere.

Inda wasu fusatattun mutane sukayi nasarar damke shi suka bashi kashi sosai wanda yayi sanadiyar mutuwarsa, mai magana da yawun ‘yan sandan,Gambo Isa yace suna nan suna kokarin kamo sauran barayin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.