Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, Adams Oshiomhole, ya yi ikirarin cewa minista da wasu gwamnoni ne ke da alhakin wahalar da ya sha a cikin jam’iyyar.
Amma, tsohon gwamnan jihar Edo bai bayyana sunan ministan da gwamnoni ba.
Yayi magana ne jim kadan bayan ganawa da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.
Taron rufe ƙofar ya faru ne a yayin da labarai suka bayyana cewa Mai shari’a Lewis Allagoa na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, ta yanke hukuncin Babbar Kotun FCT ta dakatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC.
Ya ce ya zo ne domin yi wa Buhari cikakken bayani kan abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar, kasancewar shi ne shugaban kasa. Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.