Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty international ta bayyana cewa wasu jihohin kasarnan da suka hada da Kano da Kaduna na amfani da kotun tafi da gidanka a lokacin dokar zaman gida dole suna wa mutane kwacen kudi.
Wannan ya fitone daga shugaban kungiyar reshen Najeriya, Osai Ojigbo a yayin da yake magana a wata ganawa da aka yi dashi ta yanar gizo kan ‘yancin dan Adam.
Ya bayyana cewa sun ta karbar korafi daga mutane cewa ana musu kwace ta hanyar amfani da kotun tafi da gidanka.
Yace a wasu lokutan ma mutane na gaya musu cewa ana karbar cin hanci a hannunsu. Ttun kamin fara saka dokar zaman gida muke samun irin wannan matsalar tawa mutane kwace da sunan kotun tafi da gidanka, inji Osai Ojigbo.
Ya kara da cewa doka bata bada damar awa mutum shari’a ba tare da bashi damar samun lauyan da zai bashi kariya ba.
Yace amma matsalar da ake samu shine su lauyoyi basa cikin wanda aka yadda su yi zirga-zirga lokacin da ake cikin kulle.