Wasu kafafen watsa labarai sun bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin tsohon shugaban kasa a lokacin da suka wallafa labarin kaddamar da kwamitin da zai duba yiyuwar karin albashi da shugaban yayi a jiya, me baiwa shugaban kasar shawara ta fannin sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad ya jawo hankulan wadannan kafafen da su gyara wannan kanun labarai da suka saka, a cikin wani sako daya rubuta yacewa, Muhammadu Buhari shine shugaban kasa Najeriya a yanzu.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Wannan abu ya jawowa wadannan kafafen watsa labarai Allah wadai, inda mutane suka rika cewa ko menene manufarsu ta wallafa irin wannan labari haka?
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});