Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana cewa magana dake tunzura mutane na daga cikin matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya.
Femi ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook, inda yace irin wadannan mutane masu kalaman tunzura jama’a basa magana akan manyan ayyukan da gwamnatinsu ke yi.
Yace irin wadannan malamai dama mutane suna son su samu wata dama ne kawai da kuma wani karfin iko shiyasa suke irin wadannan maganganu.
A kwanakin nan ne dai aka dakatar da limamin masallacin Apo na ‘yan majalisu dake Abuja kan maganar da yayi akan matsalar tsaro bayan harin da aka kai kan jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja.