fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Wasu mutane a jihar Ekiti sun kashe kafinta da aka yi kuskuren cewa dan fashi da makami ne

Wani kafinta dan shekaru 45, Olufalayi Obadare, ya rasa ranshi a hannun wasu mutane dake zargin cewa shi dan fashi ne a yankin Olujoda da ke Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

 

An samu rahoto cewa wasu matasa, wadanda suka hango kafinta yana yawo a unguwar da misalin karfe 5 na yamma a ranar Talata, sun kuskure shi a matsayin daya daga cikin yan fashin da ke damun yankin.
An bayar da rahoton cewa matasan sun haumasa da muggan makamai wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar shi.
Matar Obadare, Yemi, wacce ta ce mijinta, mahaifin yara uku, ya bar gidansu ranar Talata don zuwa yankin Olujoda don ganawa da wani abokin cinikinsa, ta ce cewa sam ba daidai ba ne matasan su kuskure shi a dan fashi ba tare da tabbatar da zargin na su ba.
Matar  ta bukace yan sanda da sauran hukumomin da suka dace, dan tabbatar da an gano wadanda suka aikata laifi da kuma tabbatar da adalci a cikin lamarin, ta ce, “Maigidana ya fada min cewa zai tafi Olujoda ne don neman aiki.
“Na yi mamakin lokacin da na ji an kashe shi saboda zargin, tambayar da za a masu shine, shin sun ga wani makami mai hatsari a tare dashi? Me ya sa ba su iya kai shi wurin mutumin da ya neme shi aikin ba? don sanin asalin lamarin?
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ekiti, Sunday Abutu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, ya ce,“ An fara bincike game da lamarin. ”
Abutu, wanda ya ce an ajiye gawar mamacin a cikin dakin ajiye gawarwaki, ya kara da cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Bincike ya nuna cewa rabin 'yan Najeriya zasu fada talauci a karshen shekarar 2022

Leave a Reply

Your email address will not be published.