Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi zargin cewa mutane masu fada aji suna daukar nauyin ‘yan ta’adda a jihar.
Jihar Zamfara dai ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan kwanakin nan.
A ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, ‘yan bindiga sun sace wasu dalibai mata 5 na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Lafiya da ke Tsafe a Jihar Zamfara.
Da yake mayar da martani, gwamnan jihar, Matawalle ya ce wasu manyan mutane ne ke daukar nauyin ‘yan bindigar.
Ya kuma yi zargin cewa ‘yan bindiga sun dauki mazauna jihar aiki a matsayin masu ba su bayyanan sirri.
Matawalle ya ce a bisa dalilin haka ya sa aka umarci masu rike da mukaman siyasa a jihar da su rantse da Alkur’ani cewa ba su da hannu a wannan lamarin.
Sai dai ya ce wasu manyan ‘yan siyasa a jihar sun ki yin amfani da kur’ani wajen rantsuwa.