Fitacciyar jarumar finafinan hausa na Kannywood watau Rahma Sadau ta wallafa bideyon ‘yan kasar Sin watau China suna cashewa da wakar rariya a Twitter.
Inda tace ‘yan Najeriya hadda hausawa basa kaunar funafinan Kannywood amma gashi ‘yan kasar Sin na cashewa abinsu da wakar rariya.
Wasu na kyamatar finafinan yaren Hausa, duk dacewa suma hausawa ne… A binin sin (China) suna koyar da rawa da waka irin ta Kannywood.
Wannan wakar RARIYA ce film din @sadaupictures_ wanda Director @yaseenauwal ya bada umarni… Sarki @alinuhu da @Rahma_sadau suka taka rawa. pic.twitter.com/E4mxxeEkFw
— Labaran Kannywood (@Hausafilmsnews) June 18, 2022