fbpx
Monday, March 1
Shadow

Wasu ‘yan bindiga a jihar Anambra sun harbe mutane Uku

Rahotanni daga jihar Anambra na nuni da cewa wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su waye ba sun harbe mutum uku.

‘Yan bindigar an shaida cewa sun zo ne a cikin wata Mota kirar Mercedes V.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Haruna Mohammed, ya ce rundunar ta sha alwashin kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Dan haka rundunar ta bayyana sunayen wadanda abin ya rutsa dasu kamar haka, “Izuchukwu Idemili mai shekaru 32 da, Chidi Oforma ‘mai shekaru 31 da Bongo Muoghalu’ mai shekaru 45.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *