Wednesday, December 4
Shadow

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Janar Din Sojoji a Abuja

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Janar Din Sojoji a Abuja

Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya, FCT, ta kaddamar da bincike kan wani mummunan kisan gilla da aka yi wa wani Birgediya Janar na sojojin Najeriya, Uwem Harold Udokwe mai ritaya.

DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe Janar Udokwe a babban birnin kasar ranar Asabar.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh ta fitar, ta ce an kai wa marigayin hari tare da kashe shi a gidansa na Sunshine Homes Estate da misalin karfe 3 na safiyar ranar Asabar.

Karanta Wannan  Alamomin cikin wata tara

Ta ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth C. Igweh, “ya ​​ba da umarnin gudanar da sahihin bincike kan al’amuran da suka shafi wannan abin bakin ciki.”

Kakakin ‘yan sandan ta bayyana cewa CP wanda ya jajantawa iyalan mamacin, ya kuma tabbatarwa da al-ummar cewa za a yi adalci cikin Gaggawa.

Ya bayyana cewa za a kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin tare da gurfanar da su a gaban kuliya

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *