Lamarin ya faru ne a Ibadan ranar Litinin lokacin da wasu ‘yan fashi da makami suka harbe wani mai suna Taoreed Akano.
A cewar rahoton, lamarin wanda ya faru da misalin karfe 1.20 na yamma a gaban ofishin hukumar muhalli ta jihar Oyo, rahotanni sun bayyana cewa barayin sun bi sahun Akano a lokacin da ya je cirar kudi Kimanin N150,000 da N296, 000 a bankin Guaranty Trust da ke Bodija.
A hanyar sa ta komawa, barayin wadanda suke kan wani babur sun yi nasarar budewa Akano wuta daga bisani su ka kuma tsere da baburin sa kirara Bajaj.
Wasu shaidun gani da Ido dake Ofishin hukumar muhalli sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka bayyana da cewa, sun iske gawar Akano a gefen titi kwance cikin jini nan take suka garzaya dashi zuwa Asbitin Jihar.
Haka zalika shima, Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda na Oyo, Gbenga Fadeyi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an ajiye gawar Akano a asibitin Adeoyo.