An yi garkuwa da matar da diyar Kwamishinan Muhalli na Jihar Filato, Usman Bamaiyi bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun mamaye harabar su da sanyin safiyar ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni jami’an rundunar suka bi sahun wadanda suka sace su domin tabbatar da kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su.
Babu tabbas ko Kwamishinan yana gida yayin harin. Wannan mummunan lamari ya zo ne mako guda bayan da aka sace wasu fastoci biyu a yankin.