Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a gidan kwamishinan shari’a na jihar Imo, Cyprian Akaolisa.
‘Yan bindigar sun kuma lalata gidan mahaifinsa da ke Obibi, Awo-Idemili, karamar hukumar Orsu ta jihar.
Akaolisa wanda ya tabbatar da harin, ya yi mamaki matuka, inda ya ce be san dalili da yasa akayi masu hakan ba shi da mahaifinsa.