Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kashe wani dan sanda da kuma wani dan achaba a Effurun da ke jihar Delta.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:30 na safiyar Lahadi, 5 ga watan Yuni, a Uti Junction a Effurun, karamar hukumar Uvwie ta jihar.
An ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da bindigogi kirar AK-47 mallakar dan sandan tafi da gidanka.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Bright Edafe, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar ranar Litinin, ya ce an yi awon gaba da bindiga guda daya.