A ranar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka kashe shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders’ Association of Nigeria (MACBAN) a karamar hukumar Gwagwalada da ke Abuja, Adamu Aliyu.
An kashe Aliyu ne tare da wasu hudu a kusa da kauyen Daku da ke gundumar Dobi ta karamar hukumar a ranar Alhamis.
The Nation ta gano cewa an yi garkuwa da mutane uku yayin da wasu uku suka samu raunuka.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar The Nation, sakataren MACBAN, Mohammed Usman, ya ce marigayi shugaban MACBAN tare da wasu mutane shida suna dawowa daga kasuwar Izom da ke jihar Neja a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai masa hari.
Ya ce an yi jana’izar Aliyu da wasu mutane hudu da suka hada da Saleh da Aliyu da Muhammadu da Saidu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, DSP Josephine Adeh, ta ce ba ta da labarin faruwar lamarin har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.