Wata ‘yar agaji da ke zaune a Kaduna, malama kuma tsohuwar shugabar sashin injiniyan lantarki ta Kaduna Polytechnic, Injiniya Ramatu Abarshi, diyarta da wani direban dan kasuwa an yi garkuwa da su a hanyar Kaduna zuwa Kachia a karshen mako.
Abarshi da diyarta Amira suna kan hanyarsu ne daga kauyen Mariri a karamar hukumar Kajuru inda suka je raba kayan agaji da suka hada da kayan Sallah ga yara marayu inda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Wani malami a kwalejin kimiyya da fasaha wanda ya tabbatar wa jaridar The Nation cewa ‘yan bindigar sun bi sawun su, suka kai musu farmaki tare da yin garkuwa da su a kusa da Kasuwan Magani da yammacin ranar Asabar.
Wata abokiyar wadanda aka yi garkuwa da su ta shaida wa manema labarai cewa yan bindigar sun tuntube danginsu kuma sun bukaci a biya su Naira miliyan 100 domin a sako su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya ce zai tuntubi DPO mai kula da Kasuwan Magani domin jin cikakken bayanin lamarin.