‘Wasu ‘Yan Nijeriya Sun Kama Kifi Mafi Sauri A Duniya Wanda Kudinsa Ya Haura Naira Dubu 600 Amma Sun Dafe Shi Sun Cinye
Daga Comrd Yusha’u Garba Shanga
Wasu matasa ‘yan Najeriya sun kama wani kifin ruwa mai suna Sailfish a lokacin da suke bakin aiki wurin ruwa a jihar Legas.
Daya daga cikinsu wanda Injiniyan Ruwa ne ya sanar da kame dabbar da ake kira amphibian wacce ita ce kifi mafi sauri a duniya.
Da yake magana a shafinsa na Tuwita, @Mista_YPNation ya raba hotunansu rike da kifin akan wata na’ura kamar yadda ya bayyana cewa suna amfani da shi wajen shirya barkonon tsohuwa.
A cewar yankin Facts na Afirka, cikakken girman Sailfish ya kai kimanin $1,500 a kasuwar duniya (kimanin N623,000).