fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Wasu ‘Yansanda sun bayyana dalilin da yasa suka ki bin umarnin IGP, suka bar mutane nata kwasar Ganima

Tuni dai shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP, Muhammad Adamu ya bada umarnin a kai ‘yansanda ns musamman jihohi dan su hana lalata guraren gwamnati dana kasuwanci da ake.

 

Saidai ‘yan Najeriya da dama na mamakin yanda aka bar mutane suna cin karensu babu babbaka ta hanyar fasa guraren Ajiyar kayan Abinci na gwamnati da guraren kasuwanci na mutane ana kwasar kaya.

‘Yansandan dai sun yi biris da Umarnin Gwamnati na daukar mataki akan lamarin. Wannan yasa shugaban ‘yansandan ya sake bayar da wata sabuwar umarnin amma duk a banza ‘yansandan sun ci gaba da kallon mutane na abinda suke so.

 

Wani dansanda ya gayawa, Telegraph cewa gwamnati ta yi watsi dasu hakanan suma mutanen gari da suke karewa sun hi watsi dasu. Yace akwai dansandan da ya fita aiki aka tareshi aka kashi akwai wanda suka jikkata amma kaga wani ya je ya jajanta musu?

Karanta wannan  Sanata Shehu Sani ya cewa gwamnonin da suka baiwa Buhari shawara ya sallami ma'aikatan da wuce shekara hamsi su fara kansu

 

Yace sai masu laifi wanda ‘yan iskan gari ne gasunan da bindiga suke ake daurewa gindi ana basu kulawa. Dansandan da baiso a bayyana sunansa ya ce sun barwa mutane su kare kansu.

 

Yace mahaukaci ne kawai zai rika kare mutumin da bai sonsa. Yace dansanda shine wanda aka fi zagi a kasarnan.

 

Shima wani dansandan yacs dalilin da yasa suka bar mutane shine an ce kada su yi harbi, yace kuma mutane suna sane da wannan umarni shiyasa suke abinda suke so.

 

Ya kara da cewa kuma duk wanda ya sake yayi harbi aka kamashi to za’a hukuntashi shiyasa suka bar mutane.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.